in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya bukaci gwamnatocin Afrika da su kara kaimi don hada kan nahiyar
2018-10-26 11:33:43 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo a jiya Alhamis ya bukaci gwamnatocin kasashen Afrika da su bunkasa hanyoyin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin cimma manufar tabbatar da hadin kan nahiyar.

Da yake jawabi a babban taron kungiyar ta AU game da sha'anin bunkasa tsaro, zaman lafiya, da kwanciyar hankali a karo na 9, Akufo-Addo ya ce, yunkurin dunkulewar nahiyar Afirka gu daya zai iya samun cikas, idan kasashen Afrika suka cigaba da yin sakaci da batun tsaron rayukan jama'arsu wanda ya kasance babban abin da ke damun al'ummomin nahiyar a halin yanzu.

"Babu wata kasa da za ta so yin hadin gwiwa da kasar da gidanta ya kama da wuta," ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bada labari game da kafa kungiyar tarayyar turai (EU) wanda a cewarsa kafuwarta ta taimaka matuka wajen hana yake-yake a tsakanin mambobinta, tun bayan yakin duniya na II a shekarar 1945. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China