in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu kaura 193 sun koma gida Najeriya daga kasar Libya
2018-12-07 09:44:50 cri
Hukumar dake kula da masu kaura ta duniya IOM, ta ce wasu 'yan Najeriya su 193 da suka shiga kasar Libya ta barauniyar hanya, sun amince su koma gida bisa radin kan su.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, tuni aka kwashe 'yan ci ranin zuwa gida, karkashin shirin da asusun amintattu na kungiyar tarayyar Turai EU ke baiwa tallafi.

IOM da abokan huldar ta dai na mayar da 'yan ci rani da suka amince su koma gida bisa radin kan su yankunan su, da nufin rage yawan bakin hauren dake gararanba a Libya.

Da yawa daga irin wadannan bakin haure dai na cunkushe a wasu sansanonin jami'an tsaro na killace mutanen da suka shiga Libya ba da izini ba.

Kasar Libya ta zamo wani wuri na yada zango ga dubban bakin haure dake fatan tsallakawa yankunan nahiyar Turai ta tekun Mediterranea, tun bayan da kasar ta tsunduma cikin yamutsi, biyowa bayan boren da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China