in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Cutar zazzabin shawara ta hallaka mutane 9
2018-12-06 09:31:34 cri
Rahotanni daga jihar Edo dake kudancin Najeriya, na cewa cutar zazzabin shawara ta hallaka wasu 'yan jihar 9, tun bayan bullar ta a watan da ya gabata.

Da yake tabbatar da hakan ga manema labarai, kwamishinan lafiyar jihar David Osifo, ya ce binciken da jami'ai suka gudanar ya nuna cewa, cutar ta riga ta yadu zuwa kananan hukumomin jihar 10.

David Osifo ya ce 7 daga wadanda cutar ta hallaka sun rasu ne kafin a kai su asibiti, kuma mamatan na tsakanin shekarun haihuwa 14 zuwa 20.

A ranar 24 ga watan Nuwambar da ya gabata ne dai, hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, ta fidda gargadin barkewar wannan cuta a jihar ta Edo.

Yanzu dai NCDC tare da abokan huldar ta, ciki hadda hukumar lafiya ta duniya WHO, da hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta jihar Edo, na gudanar da shirye shiryen tunkarar kalubalen yaduwar wannan cuta. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China