in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba kunbunan BeiDou na hidimar sufuri
2018-11-19 09:21:08 cri
Kasar Sin ta yi nasarar harba tagwayen taurarin dan Adam nau'in BeiDou, na ayyukan sufuri ta amfani da rokar Long March-3B. An dai harba taurarin dan Adam din ne daga tashar Xichang dake lardin Sichuan, da misalin karfe 2:07 na asubahin yau Litinin.

Taurarin dan Adam din dai sun shiga falakin su ne bayan shafe sa'o'i 3, za su kuma yi aiki tare da wasu taurarin nau'in BeiDou guda 17, da kuma wasu nau'in BeiDou mai lamba 3 wadanda ke sararin samaniya. Su ne kuma taurari na 42 da na 43 a sahun taurarin BeiDou da aka harba.

Da wannan nasara, kasar Sin ta kammala ayyukan harba taurarin nau'in BeiDou, kuma kasar na fatan amfani da nau'in BeiDou mai lamba 3, domin ba da hidimomin taswirar wurare, da tallafawa harkokin sufuri ga kasashen da shawarar nan ta ziri daya da hanya daya ta shafa, nan da karshen shekarar nan.

BeiDou sun samo sunan su ne daga sunan rukunin wasu taurari mafiya yawa a sararin samaniya bisa labarun Sinawa, an kuma fara aiki da samfuran taurarin dan Adam na BeiDou a kasar Sin ne tun daga shekara ta 2000, da kuma a yankunan tekun Fasifik a shekarar 2012. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China