in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin na fatan gamayyar kasa da kasa ta yi hadin gwiwa wajen nazarin kimiyyar rai
2018-10-27 16:04:14 cri
A yau Asabar ne aka kaddamar da taron kimiyyar rai na kasa da kasa na shekarar 2018 a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Keqiang, wanda kuma mamba ne na kwamitin dindindin na hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya mika wani muhimmin sako ga taron, inda ya nuna cewa, kimiyyar rai wadda take da nasaba da lafiya da kuma ci gaban bil Adama, ta zama wani muhimmin bangare ga dimbin kasashen duniya wajen nazarin sabbin ilmin kimiyya da kirkiro sabbin fasahohin zamani. Sakamakon haka, kimiyyar rai tana da kyakkyawar damar neman samun ci gaba da ba a taba ganinta a da ba. Yanzu kasar Sin tana aiwatar da manufar neman samun ci gaba bisa sabbin ilmin kimiyya da fasahohin zamani tare da tabbatar da kiwon lafiyar al'ummarta, sabili da haka, tana ta kokarin mai da hankali wajen nazarin kimiyyar rai, da kuma sabbin fasahohin zamani da sabbin masana'antun dake da nasaba da kimiyyar rai, ta yadda za a iya sabunta karfin neman bunkasar kasar.

Li Keqiang na fatan mahalarta taron za su kara yin musayar ra'ayoyi bisa babban jigon taro, da kuma kokarin samun matsaya daya, ta yadda za a iya samun sabbin ilmi da fasahohin zamani a fannin kimiyyar rai. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China