in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bada tallafin dala miliyan 1.5 ga Sudan ta kudu don aikin rigakafin cutar Ebola
2018-10-26 11:18:25 cri

Gwamnatin kasar Sin ta bada tallafin dala miliyan 1.5 ga kasar Sudan ta kudu domin taimaka mata wajen aikin rigakafin hana yaduwar kwayar cutar Ebola mai saurin kisa, wadda tuni ta hallaka mutane sama da 100 a makwabciyar kasar wato Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo wato DRC.

Riek Gai Kok, ministan lafiya na kasar Sudan ta kudu, ya ce, tallafin ya zo a daidai lokacin da kasar ke bukatarsa domin aikin dakile yaduwar cutar ta Ebola a yankunan dake makwabtaka da DRC.

Kok ya ce, za'a yi amfani da kudaden tallafin na kasar Sin wajen sayan motocin daukar masara lafiya da sauran kayayyakin da ake bukata don aikin bada agajin gaggawa wanda hakan zai taimakawa kasar domin tabbatar da hana bazuwar kwayar cutar mai saurin hallaka bil adama.

He Xiandong, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu, ya ce tallafin zai taimakawa ma'aikatar lafiyar kasar wajen kai daukin gaggawa da kuma hana kwayar cutar ta Ebola bazuwa a kasar Sudan ta kudun, ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin a shirye take don cigaba da tallafawa bangaren lafiyar Sudan ta kudun.

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO), kasar Sudan ta kudu na daya daga cikin kasashe 4 mafiya hadarin fargabar fuskantar yaduwar annobar cutar ta Ebola wadanda sauransu uku su ne Burundi, Rwanda, da Uganda tun bayan bullar cutar a DRC, wanda kawo yanzu ta yi sanadiyyar hallaka mutane 120 tun daga watan Agusta da ya gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China