in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta ce tana aikin samar da yanayin jan hankalin masu zuba jari daga ketare
2018-11-10 16:28:51 cri
Kasar Sudan ta kudu, ta ce tana aikin samar da kyakkyawan yanayin zuba jari, domin jan hankalin masu zuba jari na kasashen waje, a daidai lokacin da kasar ke kokarin farfado da tattalin arzikinta da ya shiga mawuyacin hali cikin sama da shekaru hudu sakamakon yaki.

Sakatare Janar na hukumar kula da zuba jari ta kasar, Abraham Maliet Mamer, ya shaidawa manema labarai a birnin Juba cewa, kofar kasar a bude take, kuma a shirye take, ta karbi jarin da zai farfado da tattalin arzikinta.

Ya ce kofofin kasar sun dade a rufe, yanzu kuma lokaci ya yi na magana da babbar murya kuma a bayyane cewa, kasar ta shirya karbar jari.

Sudan ta Kudu dai ta dogara ne da samar da man fetur, wanda ke samar da kaso 98 na kudaden da take kashewa, kuma a baya bayan nan ne ta sanar da yunkurinta na bunkasa samar da man da ya gamu da tsaiko biyo bayan rikice-rikice, al'amarin da ya sa yawan man da kasar ke samarwa ya ragu zuwa kasa da ganga 165,000 a kowacce rana, daga ganga 350,000 a shekarar 2012.

Sudan ta Kudu ta shirya karbar taron zuba jari kan man fetur da iskar gas karo na 2, a ranekun 21 da 22 na watan nan a birnin Juba. An yi taron na farko ne a watan Oktoban bara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China