in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afrika za su halarci bikin wanzar da zaman lafiyar Sudan ta kudu
2018-10-31 09:39:33 cri
A kalla shugabannin kasashen Afrika 4 ne za su halarci wani muhimmmin bikin tabbatar da zaman lafiyar Sudan ta kudu wanda aka shirya gudanarwa a yau Laraba a Juba.

Michael Makuei Lueth, ministan yada labaran Sudan ta kudun ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Juba, ya ce shugabannin da za su halarci bikin daga shiyyar suna cikin kasashe mambobin kungiyar ci gaban gabashin Afrika (IGAD), kana sun tabbatar da cewa za su halarci bikin tabbatar da zaman lafiyar a wani mataki don kawo karshen yakin basasar kasar wanda aka shafe sama da shekaru 4 ana fuskanta.

Ya ce shugaba Yoweri Museveni na Uganda, da shugaban Sudan Omar al-Bashir, da na Somalia Mohamed Abdulahi Mohamed da kuma shugabar kasar Habasha Sahle-Work Zewde dukkansu za su halarci bikin.

Ya kara da cewa, daga cikin muhimman mutanen da ake sa ran za su halarci bikin sun hada da firaiministan kasar Masar Mostafa Madbouly da ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita, da kuma wakilai daga kasashen Najeriya da Afrika ta kudu.

Haka zalika, madugun 'yan adawar kasar Riek Machar wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe tare da shugaban kasar Salva Kiir a watan Satumba a kasar Habasha za su halarci bikin wanzar da zaman lafiyar bayan da ya shafe sama da shekaru 2 yana gudun hijira a kasashen waje. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China