in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ta bukaci gwamnatin Somaliya da ta kara azama wajen shirin farfadowar kasar
2018-12-11 10:18:35 cri
Asusun bada lamuni na duniya (IMF), a jiya Litinin ya bukaci gwamnatin kasar Somaliya da ta kara himma wajen aiwatar da sauye-sauye a tsarin farfado da ci gaban kasar na tsawon lokaci da kuma manufofin gina kasar.

Tawagar hukumar ta IMF wadda Mohamad H. Elhage ya jagoranta, inda suka ziyarci kasar Kenya tsakanin ranar 1 zuwa 6 ga watan Disamba domin wata ganawa da jami'an hukumar kudi na kasar Somaliya da kuma sabunta shirin raya kasar wato (SMP), na watanni 12 tsakanin watan Mayun 2018 zuwa watan Afrilun shekarar 2019, ya ce IMF a shirye take ci gaba da tallafawa ajandar sauye-sauyen na kasar Somaliya da kuma bunkasa hanyoyin ci gaban kasar ta hanyar bada taimakon kwararru da kuma samar da horo.

"Duk da irin matsanancin yanayin da ake ciki, ayyukan SMP yana da matukar karfi," in ji wata sanarwa daga tawagar.

Tawagar jami'an na IMF sun yi maraba da aniyar gwamnatin Somaliya wajen ci gaba da inganta ayyukan shirin na SMP na tsawon shekara guda wato shekarar 2018 da 2019 ta hanyar fadada hanyoyin samar da kudaden shiga daga sabbin matakan tara haraji da kuma takaita yadda ake kashe kudaden gudanarwar yau da kullum na shirin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China