Ma'aikatar shari'ar kasar da shirin raya kasashe na MDD (UNDP) ne suka sanya hannu kan shirin na PIP, da nufin kara karfin hukumomin gwamnati na yaki da cin hanci da karfafa kula da dukiyar al'umma.
A jawabinsa yayin bikin kaddamar da shirin da MDD ke marawa baya, ministan shari'a na kasar Somaliya Hassan Hussein Haji ya bayyana cewa, kasarsa na shirin kara hukumar yaki da cin hanci, don haka suna bukatar sakatariya, da horaswa da ma taimako a dukkan fannoni.
Ya kuma bayyana jerin matakan da gwamnati ke dauka na jaddada kudurinta na yaki da cin hanci da rashawa da gudanar da ayyuka a bayyane domin gina hukumomin da za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya ce, musamman ma aikin zai karfafa gudanar da ayyuka bisa doka a wasu muhimman hukumomin kasar, kamar ofishin babban mai binciken kudi na kasar da sauransu. (Ibrahim)