Rahotanni daga yankin sun ce, mayakan Al Shabab ne suka kaddamar da hari kan wata cibiya, ta wani malamin addinin musulunci mai suna Sheikh Abdiweli Ali Elmi, bayan da mayakan kungiyar suka zarge shi da furta wasu kalamai na tozarta Annabi Mohammad.
Tuni kuma Al-Shabab ta ayyana daukar alhakin kaddamar da wannan hari.