Nicholas Haysom, wanda shi ne manzon musamman na Sakatare Janar na MDD a Somalia, ya yi kira da a wareware rikicin da ake a garin Tukaraq na yankin Sool da ake takkadama a kai, cikin ruwan sanyi.
Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, jami'in ya ce ya gana da shugabannin yankunan biyu, inda suka tattauna kan batutuwa daban-daban, ciki har da yankin da ake rikici a kai.
An fara samun rikici a Tukaraq ne tun cikin watan Junairu, bayan dakarun Somaliland sun yi arangama da takwarorinsu na Puntland, dangane da neman iko da yankin na Sool.
Jihohin biyu na Somalia, sun sha karawa tun shekarar 2002 dangane da neman iko da yankunan arewacin kasar da suke takkadama a kai. (Fa'iza Mustapha)