"Dakaru na Amurka sun kaddamar da hare haren ta sama ne bayan da sojojin na Amurka da dakarun kawance suka fuskanci matsin lamba na kai musu hari. A halin yanzu mun tantance wannan harin ta sama ya yi sanadiyyar hallaka mayakan 'yan ta'adda 4 ba tare da kashe farar hula ba," in ji dakarun sojin Amurka dake Afrika (AFRICOM) cikin wata sanarwa.
Dakarun sojojin sun sanar da cewa, sun yi kokarin hana mayakan na al-Shabab samun sukuni wajen daura damara da kuma kaddamar da hare hare kan mutanen kasar Somalia.
"Musamman, kungiyar sun yi amfani da yankunan kudanci da tsakiyar Somali wajen shiryawa da kuma kaddamar da harin ta'addanci kai tsaye, da sace kayayyakin jin kai, da kwace kayayyakin jama'a domin su samu damar gudanar da ayyukansu, da shirya cibiyoyin ayyukan ta'addanci," in ji AFRICOM. (Ahmad Fagam)