Wani jami'in 'yan sanda da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an gano karin gawawwaki karkashin baraguje, lamarin da ya kai ga karuwar wadanda suka mutun zuwa 50. Yana mai fargabar cewa, watakila akwai karin mutane da kasa ta danne, amma dai suna iya bakin kokarinsu na ganin sun gano wadanda suka bace.
A ranar Jumma'a da rana ne dai wasu manyan bama-baman suka tashi a kusa da mahadar kilomita 4, inda ake zargin maharan Al-shabaab da auna otel din Sahafi da 'yan siyasa suka fi zama kana wani wuri mai tsaro da a baya 'yan jaridu ke yawan zuwa don dauko rahotanni game da yakin basasar kasar ta Somaliya.
Hotunan daga wurin da lamarin ya faru na nuna baragujen motoci warwatse a kan hanyar. Sai dai kuma MDD da wasu kasashen ketare sun yi Allah wadai da hare-haren, wadanda ke zuwa 'yan watanni bayan da kasar Somaliyar ke cika shekara guda da harin bam din da aka kai cikin wata babbar mota a ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2017, harin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 500.
A halin da ake ciki, ita ma tawagar kungiyar tarayyar Afirka dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya(AMISON) ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a kan otel din na Sahafi da ma hedkwatar leken asirin kasar dake birnin Mogadishu mai fama da tashin hankali.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Asabar a birnin Mogadishu, tawagar ta AMISON ta lashi takwabin karfafa sintiri tare da gwamnatin Somaliya da nufin murksuhe 'yan ta'adda da ma ragowar kungiyoyin 'yan tawaye.(Ibrahim)