in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda: Jirgin ruwa ya kife da baki mahalarta bikin aure 19 a Najeriya
2018-12-03 10:26:07 cri
Hukumar 'yan sanda a Najeriya sun sanar da cewa kimanin baki mahalarta bikin daurin aure su 19 ne aka tabbatar sun nitse a kogi yayin da jirgin ruwan dake dauke da su ya kife da yammacin ranar Asabar a yammacin Najeriya.

Lamarin dai ya auku ne a lokacin da bakin mahalarta bikin auren gargajiyar suke kokarin komawa gidajensu bayan kammala shagalin bikin, inda kwale-kwalen da suke ciki ya kife a kogin Niger, dake yankin Lafiagi a yammacin jihar Kwara.

Jami'an 'yan sanda da sauran majiyoyi sun sanar da cewa, fasinjoji 21 ne a cikin kwale-kwalen a lokacin da ya kife. Kuma mutane biyu ne kadai suka tsira a hadarin.

Masu aikin ceto sun riga sun tsamo gawarwakin mutanen 19.

Ajayi Okasanmi, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kwara, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hukumar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro a yankin sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin da ya haddasa faruwar hadarin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China