in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da ginin titin mota da zai hade jihohin Najeriya 3
2018-11-23 09:37:42 cri
A jiya Alhamis ne aka kaddamar da aikin ginin titin mota, da gyaran wani sashe na titin birnin Abuja zuwa jihohin Nassarawa da Benue a tarayyar Najeriya, aikin da bankin EXIM na kasar Sin zai samar da bashin kaso mafi tsoka na kudaden gudanar da shi.

Kamfanin kasar Sin na gine gine mai suna China Harbor Engineering Company ne zai gudanar da aikin, wanda zai lashe zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan 500.

Bisa tsarin aikin, gwamnatin Najeriya za ta samar da kaso 15 bisa dari na kudanden, yayin da bankin EXIM na Sin zai samar da rancen ragowar kaso 85 bisa dari na kudaden aikin.

Rahotanni sun ce aikin ya kunshi ginin babbar hanyar birnin Abuja zuwa Keffi mai tsawon kilomita 5.4, wadda za ta hade birnin Abuja fadar mulkin kasar da jihar Nasarawa mai makwaftaka, sai kuma aikin fadada titin Keffi zuwa Akwanga zuwa Lafia zuwa Makurdi, wanda zai hade jihohin Nasarawa da Benue mai tsawon kilomita 221.8.

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin a garin Keffi na jihar Nasarawa, ministan ayyuka da gidaje na tarayyar Najeriya Babatunde Fashola, ya ce aikin wani muhimmin mataki ne na hade sassan al'ummun dake shiyyar.

Shi ma a nasa jawabin, gwamnan jihar Nassarawa Umaru Tanko Al-Makura, cewa ya yi aikin zai rage tsayin tafiya tsakanin jihar sa da makwaftan jahohi dake kewayen ta, kana zai taimaka wajen rage yawan hadurra da ake gamuwa da su, sakamakon matsi da titin ke da shi a halin yanzu.

Manyan jami'an gwamnatin Najeriya, da suka hada da gwamnoni, ministoci, da 'yan majalissar dattijai da dama, da ma sauran al'ummun yankin sun halarci bikin kaddamar da aiki. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China