in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin ranar yaki da cutar Noma a Najeriya
2018-11-21 10:38:44 cri
Gwamnatin Najeriya ta shirya bikin ranar fadakarwa, game da cutar Noma dake haddasa tauyewar wasu halittun jikin bil Adama a jiya Talata, domin fadakar da al'ummar kasar game da cutar, da kuma matakan kandagarkin ci gaba da yaduwar ta.

A bara ne dai gwamnatin kasar ta fara gudanar da wannan biki na fadakarwa, wanda mahukuntan kasar suka tsara, a matsayin daya daga hanyoyin kawar da ita.

Da yake tsokaci yayin bikin, karamin minista a ma'aikatar lafiya na tarayyar Najeriya Osagie Ehanire, ya ce gwamnati da abokan huldar ta, kamar hukumar lafiya ta duniya WHO, da likitocin dake aikin jin kai na kasa da kasa ko "Medecins Sans Frontieres" sun amince da tasirin fadakarwa, a fagen yaki da yaduwar cutar ta Noma a Najeriya, da ma sauran kasashen yammancin Afirka inda take ci gaba da bazuwa.

Mr. Ehanire ya ce Najeriya ta fara samun nasarori a yakin da take yi da wannan cuta, bayan da ta fara aiwatar da manufofin hukumar WHO masu nasaba da hakan.

Cutar Noma, wadda kuma a kan kira "Cancrum Oris" a Turance, na kama mutum ne ta hanyar wasu kwayoyin cuta dake fakewa a sassan baki, ta kuma fi kama yara kanana, da wadanda ba sa tsaftace bakin su yadda ya kamata, inda take cinye sassan baki da kewayen sa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China