Kakakin Gwamnatin kasar Micheal Makuei, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya a birnin Juba cewa, Gwamnatin ta kuduri niyyar samar da zaman lafiya, duk da barazanar da Amurka ta yi na sanyawa manyan jami'an shugaba Salva Kiir takunkumi.
Jawaban nasa na zuwa ne a lokacin da kwamitin sulhu na MDD za ta kada kuri'ar amincewa da kakabawa wasu manyan jami'an gwamnati takunkumi, ciki har da tsohon kwamandan sojin kasar, a yau Alhamis.
Rikicin kasar Sudan ya shiga shekararsa ta 5. Rikicin dai, ya barke ne a shekarar 2013, bayan sojoji magoya bayan shugaba Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar sun gwabza fada da juna. Miliyoyin fararen hula na kasar ne suka tsere kasashe makwabta don neman mafita, yayin da rikicin ke kara kamari duk da yunkurin al'ummomin kasashen waje na kawo karshensa. (Fa'iza Mustapha)