in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta shirya tattaunawa da shugaban 'yan adawa
2018-06-05 09:27:21 cri

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya bayyana aniyar gwamnatinsa, ta tattaunawa da dadadden mai adawa da gwamnatinsa, kuma tsohon korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Litinin, kakakin shugaban kasar Ateny Wek Ateny, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, shugabannin Sudan ta Kudu sun amsa kiran kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD, game da bukatar ganawar kai tsaye da Mr. Machar.

An dai kira taron sassan biyu ne, bayan da aka gaza cimma matsaya a taron manyan jami'ai daga sassa daban daban masu rajin ganin an kawo karshen danbarwar siyasar kasar ta Sudan ta Kudu, taron da ya gudana a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Idan dai wannan shiri na shawarwari ya tabbata, zai ba da dama a karon farko da sassan biyu za su gana da juna ido da ido, tun bayan da Machar ya tsere wa kasar a watan Yulin shekarar 2016, lokacin da fada ya barke tsakanin magoya bayansa da dakarun gwamnatin kasar. An ce ana yi wa Mr. Machar daurin talala a kasar Afirka ta Kudu.

Tun a shekarar 20013 ne Sudan ta Kudu ta fada yakin basasa, lamarin da ya jefa jaririyar kasar cikin halin jin kai mafi tsanani, yayin da kimanin 'yan kasar miliyan 4 suka tsere wa gidajensu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China