Kakakin hukumar sojan kasar Masar Tamer El-Refai, ya fadi haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da manema labaru, inda ya ce an gudanar da dukkan ayyukan yakar ta'addanci ne a wuraren da suke waje da unguwannin jama'a, sun kuma samu goyon baya daga wajen mazauna wurin.
A shekaranjiya Litinin ne, shugaba Abdel Fattah al Sisi na Masar, ya sa hannu kan umurnin kara watanni 3 kan wa'adin dokar ta baci da aka kafa a fadin kasar a watan Aflilun shekarar 2017.
An kaddamar da "matakin Sinai na shekarar 2018" ne a ranar 9 ga watan Faburairun bana, domin dakile kungiyoyin ta'addanci da 'yan ta'adda, wadanda ke zaune a tsibirin Sinai. (Sanusi Chen)