in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya na sa ran samun bunkasar tattalin arzikin daga jarin dala miliyan 600 na bangaren tama da karafa
2018-12-10 09:45:32 cri
Gwamnatin Nijeriya ta ce tana sa ran inganta tattalin arziki bisa wani jari na dala miliyan 600 na sarrafa tama da karafa a kasar.

Sanawar da ministar kudin kasar Zainab Ahmed ta fitar, ta tabbatar da cewa, gwamnati ta cimma yarjejeniya da wani kamfanin hakar ma'adinai na Afirka wanda zai zuba jari a bangaren hakar ma'adinai da karafa.

Manufar yarjejeniyar ita ce, sake tsarin bangaren hakar ma'adinai na kasar. Kusan shi ne jari mai yawa na farko da aka zuba a bangaren cikin sama da shekaru 20, wanda zai samar da guraben aikin yi na kai tsaye 3,500.

Ta kara da cewa, ana sa ran aikin wanda zai kai metric ton 5.4 a shekara, zai samar da raya masana'antu da al'umma, da samar da lantarki da maye gurbin shigar da kayayyaki kasar da sauransu.

Tashar sarrafa karafan za ta samar da wutar lantarki megawatt 36 ga turakar lantarki na kasar, wanda zai bunkasa lantarkin da yanzu ake samu domin sauran ayyukan kasuwanci da bunkasa sauran masana'antu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China