Bayanai tsakanin watannin Junairu da Nuwamba da cibiyar takaita yaduwar cutuka ta kasar ta tattara, sun bayyana cewa mutane 3,016 ake zargin sun kamu da cutar tsakanin wancan lokaci.
Tun bayan gano bullarta a ranar 1 ga watan Janairu, an samu barkewar cutar mai haifar da matsanancin zazzabi da zubar jini, a jihohi 22 da kananan hukumomi 90 na kasar.
Kakakin cibiyar Chimezie Anueyiagu, ya shaidawa manema labarai a birnin Abuja cewa, adadin wadanda cutar ta kashe kawo yanzu ya kai kaso 22.6 bisa 100.
Ya kara da cewa, yanzu haka akwai shirye-shirye dake gudana na bitar matakan da ake amfani, tare da samar da wani muhimmin tsari da zai shafe tsawo shekaru 5 domin dakile cutar a Nijeriya.
Kakakin ya ce cibiyar da hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya WHO, na bincike domin gano ko akwai wata dabbar dake yada kwayar cutar.
Kasashen yammacin Afrika da suka hada da Ghana da Benin da Liberia da Saliyo ne suka ba da rahoton bullar zazzabin na lassa a bana. (Fa'iza Mustapha)