in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Annobar 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Kwato Roka Da Bindigu A Zamfara
2018-11-28 08:45:10 cri

Rundunar 'yan Sanda na jihar Zamfara sun samu nasarar kwato manyan bidiga biyu da bama bamai daga hanun 'yan ta'adda a wani farmaki ca aka yi da su a karamar hukumar Tsafe.

Da yake yi wa 'yan jarida jawabi a kan nasarorin rundunarsa, Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Usman Belel, jami'ansa sun dakile wani mummuna hari da 'yan ta'adda suka shirya in da suka kwace wadanna makaman a kauyen Hayin Alhaji.

Ya kuma kara da cewa, farmakin da suka yi ya taimaka wajen tsirar da rayuwar jama'a da dama, hare haren a baya ya yi sanadiyyar mutuwar jama'ar da basu jib a basu gani ba. Daga nan ya kuma ce, sun samu nasarar kwace bindiga kirar AK 47 guda 7 da kuma albarushai guda 9 daga hannun 'yan ta'addan a lokacin da aka yi arba da su.

Kamishina 'yan sanda Belel ya kuma bayyana cewa, sun samu nasara cafke 'yan ta'adda da dama ta hanyar amfani da bayanan sirri, abin day a taimaka wajen dakile harkokin nasu a fadin jihar.

Ya kuma kara da cewa, ana nan kuma ana aiki a kan bayanan da suke fitowa daga hannun masu basu bayanan sirri don ci gaba da dakile ayyukan 'yan ta'adda a fadin jihar gaba daya.

Daga nan kuma ya kara da cewa, a halin yanzu sun sake salo da tsarin yaki da ta'addancin da suke yi a jihar ta yadda zai dai dai da barazanar da aka fuskanta.

Ya kuma bukaci sarakuna gargajiya da manyan mutae a cikin al'umma da su ci gaba dab a 'yan sanda dukkan hadi kan da ya kamata don samumn nasara a yakin da ake yi da 'yan ta'addan.(Labari daga Leadership)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China