in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure 120 da suka nemi koma gida Nijeriya ne aka mayar daga Libya
2018-11-11 16:05:46 cri
Hukumar kula da kaura ta IOM ta ce bakin haure 'yan Nijeriya 120 aka mayar gida daga kudancin Libya, bayan sun bukaci hakan da kansu.

Sanarwar da IOM ta fitar, ta ce da taimakon hukumomin tsaro na yankin kudancin Libya, hukumar ta yi nasarar mayar da bakin haure 'yan Nijeriya 120 zuwa gida, karkashin asusun tallafi na Tarayyar Turai.

Hukumar ta ce wannan ne karon farko da jirgin bakin haure ya tashi kai tsaye daga kudancin Libya, saboda tabarbarewar yanayin tsaro.

Dubban bakin hauren da aka ceto daga teku ko wadanda jami'an tsaro suka tsare ne suka cika matsugunan na su dake Libya.

Hukumar IOM na gudanar da wani shirin kwashe bakin hauren dake watangarari a Libya, wadanda suka nemi komawa kasashensu na asali da kansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China