in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar raya fasahohi ta Najeriya ta gudanar da ranar kasar Sin
2018-11-22 09:29:47 cri
Hukumar raya fasahohi ta Najeriya NCAC, ta gudanar da ranar kasar Sin a jiya Laraba, a wani bangare na bikin kasa da kasa, na nune nunen kayayyakin zane zane, da fasahohin sassaka karo na 11, wanda ke gudana a birnin Abuja, fadar mulkin kasar.

Hukumar ta NCAC, ta ce ta ware ranar musamman domin nuna wasu daga al'adun kasar Sin masu kayatarwa, ciki hadda rawar dabbar Dragon, wadda daliban sakandare na wasu makarantun Najeriya suka gudanar, domin nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin ta fuskar musayar al'adu.

Da yake tsokaci game da hakan, jami'i mai lura da harkokin raya al'adu a ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Li Xuda, ya ce za a ci gaba da bunkasa sha'anin musayar al'adu tsakanin kasashen biyu, matakin da ko shakka ba bu, zai dada inganta hadin gwiwar dake tsakanin su.

Li ya ce ware ranar kasar Sin, a yayin bikin na bana mafarki ne da ya tabbata, ya kuma nuna irin jajircewar mahukuntan Najeriya a fannin bunkasa musayar al'adu da Sin.

Bikin na bana na mako guda, na da taken "sada ayyukan fasahohi da sassaka na Najeriya da sauran duniya". (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China