in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sake kakabawa Iran takunkumin da aka dage mata karkashin yarjejeniyar nukuliyar kasar da aka cimma
2018-08-07 10:01:38 cri

A jiya Litinin ne gwamnatin Amurka ta sanar cewa, za ta sake kakabawa kasar Iran takunkumin da aka dage mata karkashin yarjejeniyar nukuliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015, a wani mataki na kara matsawa kasar lambar.

Sai dai kuma a martanin da ya mayar shugaba Hassan Rouhani na Iran ya ce, Iraniyawa za su yi kokarin ganin Amurka ta yi dan da-na-sani game da sake kakabawa kasar takunkumi.

Wani babban jami'i a gwamnatin Trump da ya bukaci ya sakaye sunansa, ya shaidawa manema labarai ta kafar bidiyo cewa, kashin farko na takunkumin da zai fara aiki da misalin karfe 12:01 na daren yau Talata, ya shafi takardun kudaden Amurka da kasar ta Iran take saya, da bangaren kasuwancin zinare da sauran karafa masu daraja da kuma yadda ake amfani da ma'adinin graphite da karafa da sanholo da manhajan da ake amfani da su a masana'antun sarrafa kayayyaki.

Haka kuma takunkumin zai shafi yadda ake hada-hadar Rial na kasar da basussukan waje da bangaren harhada motoci na kasar.

A watan Mayun wannan shekara ce dai shugaba Trump na Amurka ya janye kasarsa daga yarjejeniyar nukuliyar ta Iran, lamarin da ya haifar da suka daga kasashen duniya, da ma baraka tsakanin kasashen turai. Wasu manyan kawayen Amurka dake yankin turai na kokarin kare yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015 daga rugujewa.

Duk da bore da hakan ya haifar daga kawayen Amurkar dake turai, jiya Litinin shugaba Trump ya sanya hannu kan wani umarnin shugaba don aiwatar da wannan takunkumi, yana mai cewa, manufar Amurka game da yarjejeniyar nukuliyar kasar ta Iran, ta shafi tantance yadda ake tafiyar da mulkin kasar da ma tasirinta Iran din a shiyyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China