A watan Mayun bana ne, shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar ta nukiliyar Iran. A watan Agusta kuma, ya sake sanyawa Iran din takunkumi a fannonin hada-hadar kudi da karafa da ma'adinai da motoci da sauransu. Shugaban na Amurka ya kuma bayyana cewa, za a kara mayar da sauran takunkuman a watan nan na Nuwanba.
Da take mayar da martani cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, ma'aikatar harkokin wajen Iran, ta ce kasar ba ta damu da takunkuman da Amurka za ta saka mata a fannonin fitar da man fetur da tsarin bankuna ba, tana mai cewa, Amurkar ta yi hakan ne don tsorata ta, sai dai hakarta ba ta cimma ruwa ba, domin kasar na da karfin raya tattalin arzikinta da tabbatar da rayuwar jama'arta bisa kowanne irin yanayi. (Zainab)