in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Amurka ta sanar da sanyawa Iran sabon takunkumi
2017-09-15 10:57:08 cri
Jiya Alhamis ne, ma'aikatar kudi ta kasar Amurka ta sanar da sanya takunkumi ga kamfanoni 4 da wasu daidaikun mutane 7, bisa zarginsu da goyon bayan shirin kasar Iran na raya makamai masu linzami da kuma yiwa tsarin sha'anin kudi ta Intanet kutse

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewa, wadanda wannan takunkumi zai shafa sun hada da kamfanoni biyu na kasar Iran, da kamfanonin biyu na kasar Ukraine, da masana na'urar kwanfuta 'yan kasar Iran 7. Shi dai wannan takunkumin,zai haramta musu taba kadarorinsu da ke cikin kasar Amurka, sa'an nan za a hana Amurkawa yin duk wata huldar cinikayya da su.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China