in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi barazanar sanyawa Iran takunkumi mafi muni
2018-05-22 10:18:22 cri

Jiya Litinin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, idan kasar Iran ba ta sauya manufarta ba a yanzu, Amurka za ta sanya mata takunkumi mafi muni.

A cikin jawabinsa a asusun kwararru na Heritage Foundation na Amurka a wannan rana, Pompeo ya ce, manufar da gwamnatin Iran take bi a yanzu ba ta da amfani, kuma ba za a amince da ita ba. Amurka za ta matsa mata lamba ta fuskar hada-hadar kudi, irin wanda ba a taba ganin irinsa a baya ba. Har ila yau ya gabatar wa Iran bukatu a fannoni guda 12, a matsayin sharuddan dakatar da takunkumin. Pompeo ya kuma kara da cewa, idan Iran ba za ta sauya manufarta ba, tabbas Amurka za ta fitar da wasu matakai daya bayan daya. Kuma muddin aka kammala fitar da matakan baki daya, za su kasance matakan takunkumi mafiya muni a tarihi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China