in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar makamashi ta duniya za ta taimakawa Afrika wajen samar da makamashi mai tsabta
2018-12-07 11:39:52 cri

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta ce za ta taimakawa Afrika wajen samar da kasuwar makamashi mai tsabta ta bai daya a nahiyar.

Adnan Amin, darakta janar na hukumar kula da makamashi mai tsabta ta kasa da kasa (IRENA), ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, sun riga sun fara bada horo ga jami'an tafiyar da makamashi na kasashen Afrika game da yadda zasu tsara dokokin da suka shafi ta'ammali da makamashi mai tsabta a Afrika.

"Mun yi amana cewa, samar da kasuwar bai daya ta makamashi mai tsabta zata samar da jari mai girma wajen samar da makamashi mai tsabta a Afrika," Amin ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da shirin dabarun inganta lantarki na kasar Kenya.

Amin ya ce samar da kasuwar makamashi mai tsabta wadda zata hade nahiyar zai taimaka wajen saukaka farashi da kuma samar da ingantaccen lantarki ga al'ummar Afrika.

Ya ce samar da kasuwar bai daya ta makamashi mai tsaba wani bangare ne na shirin bunkasa samar da kayayyakin more rayuwa karkashin sabon shirin nan na kungiyar tarayyar Afrika na raya kasashen nahiyar wato (NEPAD) a takaice.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China