in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani: Zuba jari a bangaren makamashin da ake iya sabuntawa ya dace ga ci gaban Najeriya
2018-11-28 09:08:38 cri

Wani masani a fannin makamashi mai suna Yemi Kolawale, ya bayyana cewa, zuba jari mai tarin yawa a fannin makamashin da ake iya sabuntawa a Najeriya, zai taimaka ga ci gaban masana'antu da ma tattalin arzikin kasar.

Masanin wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da manema labarai a birnin Legas, ya ce, irin wadannan jari za kuma su taimaka wajen inganta makamashin da kasar ke bukata, kasancewar makamashi na daga cikin abubuwan da kasashen nahiyar da tattalin arzikinsu ke matukar bukata, saboda ba sa gurbata muhalli.

Yemi Kolawale ya ce, hanyoyin makamashin da ake amfani da su, ba sa biyan bukatun kasar a halin yanzu, don haka zuba jari a fannin makamashin da ake sabuntawa shi ne kadai zai magance matsalar makamashi da kasar ke fama da ita.

Ya ce, hanyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana, za su iya cike gibin makamashin kasar, su kuma cika burin kasar na raya masana'antunta.

Yanzu haka dai Najeriya na samun wutar lantarkinta ne ta hanyar amfani da gas da kuma ruwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China