in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha ta kaddamar da cibiyar sarrafa shara dake samar da makashi ta farko a Afrika
2018-08-20 11:42:57 cri
A jiya Lahadi kasar Habasha ta kaddamar da kamfanin sarrafa shara dake samar da makamashi na farko wanda ya samu halartar manyan jami'an kasar da wakilan diplomasiyya na kasashen waje.

Aikin kamfanin sarrafa sharar dake samar da makamashi, wanda gwamnatin kasar Habashan ta samar da kudaden aikin, ana saran zai iya sarrafa shara kimanin ton 1,400 a kowace rana.

Aikin, wanda aka gudanar a Addis Ababa, kamfanin samar da lantarki na kasar Sin (CNEEC) shi ne ya gudanar da aikin.

Da yake jawabi a lokacin bikin kaddamar da aikin, shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome yace zuba jari a fannin makamashi muhimmin aiki ne wanda zai taimakawa kasar Habashan wajen cimma nasarar zama kasa mai tsabataccen muhalli wadda ke da cigaban masana'antu da ma matsakaicin kudin shiga nan da shekarar 2025.

A matsayinsa na kamfanin sarrafa shara dake samar da makamashi irinsa na farko a Afrika, kammala aikin da fara gudanar da aikin kamfanin babbar nasara ce in ji shi, zai kasance a matsayin tushen raya birane a Addis Ababa, na kasar Habasha da Afrika.

Samar da dawwamamman cigaba da kyautata muhalli suna daga cikin manyan jigon hadin gwiwar Sin da Afrika. Kasar Sin tana tallafawa kasashen Afrika wajen cimma nasarar samun dauwamammen ci gaba amma ba tare da gurbata muhalli ba, in ji shi. Ya ce muna cigaba da shiga ayyukan samar da makamashi mai tsabta, kare namun daji, da kyautata muhalli da aikin gona da kuma raya birane na zamani.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China