in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci a kara hadin gwiwa kan makamshi tsakanin Sin da Afrika
2018-05-15 10:13:34 cri

Mahalarta taro kan kalubalen lantarki a Afrika da aka yi a Addis Ababan Habasha jiya Litinin, sun bukaci a kara hadin gwiwa kan makamashi tsakanin kasar Sin da Afrika, domin taimakawa nahiyar samun makamashin da take bukata.

Wata kungiya ta kasar Sin, mai rajin raya makamashi da tabbatar da dorewar ci gabansa a duniya ce, ta shirya taron da aka yi kan 'hada turaku domin samun dorewar lantarki a Afrika'.

A cewar wakilin kasar Sin a kungiyar tarayyar Afrika AU Kuang Weilin, a shirye kasar Sin take ta yi aiki da tarayyar da mambobinta 55, domin cimma bukatun al'ummar nahiyar miliyan 600, dake rashin lantarki wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ya ce, hadin gwiwa kan makamashi a nahiyar zai inganta dunkulewar tattalin arzikinta, da inganta rayuwar al'ummarta, tare da bayyana damarmakin cinikayya tsakanin kasashenta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China