Guitouni ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron karawa juna sani na kasa da kasa da aka shirya game da makamashin bola jari, makamashi, da samar da abinci wanda aka bude a ranar Lahadi a birnin Algiers na kasar.
Guitouni ya lura cewa, kasar Algeria tana matukar amfana daga dunbun albarkatun dake karkashin kasa, ya kara da cewa, ma'aikatarsa tana yunkurin fadada shirin hako albarkatun mai da iskar gas.
Ministan ya bayyana cewa, kasar tana bukatar samar da ruwan sha mai tsabta, sakamakon karuwar yawan jama'a da kuma yadda ake samun cigaba a tsarin rayuwar jama'a. Haka kuma albarkatun ruwa wani babban jigo ne wajen bunkasa harkokin noma da bangaren masana'antu.