in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana kimiyya sun bukaci a samar da dokokin kula da makamashi mai tsafta
2018-03-10 13:26:26 cri

Masana kimiyya sun yi kira ga gwamnatocin Afrika, su samar da dokokin da za su kare tare da kula da makamashi mai tsafta a nahiyar

Daraktan zartarwa na cibiyar nazarin manufofin fasahar Afrika Nichols Ozor, ya ce samar da ci gaba ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta na da damar yin kyakkyawan tasiri wajen inganta tattalin arzikin galibin kasashen Afrika.

Da yake jawabi ga wani taron karawa juna sani kan samar da ci gaba ta hanyar makamashi mai tsafta, Nichols Ozor ya ce ba zai yiwu a yi amfani da damarmakin ba, idan babu dokoki da za su kare sabon bangaren.

Ya kuma ce ciyar da makamashi mai tsafta gaba na da muhimmiyar dama ta samar da ci gaban tattalin arziki ta ko wace fuska a nahiyar, a don haka akwai bukatar samar da dabaru da tsare–tsaren amfani da damarmakin.

A cewar masana kimiyya, kasashe kamar su Rwanda da Habasha da Kenya da Afrika ta kudu, sun riga sun samar da tsarin da za su bi wajen yin amfani da makamshi mai tsafta don samun dorewar tattalin arzikinsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China