A jiya ne al'ummar Nijar suka yi bikin karamar sallah bayan kawo karshen azumin watan Ramadan. A birnin Yamai, hedkwatar mulkin kasar, dubban musulmi ne ciki har da shugaban kasar Issoufou Mahamadou tare da rikiyar mambobin gwamnatin Nijar da kuma jakadun kasashe musulmi dake Nijar suka yi tururuwa zuwa babban masallancin Kaddafi don halartar sallar Idi
Bikin karamar sallah a Nijar ya zo a daidai lokacin da mutane suke fama da talauci da kuma tsadar rayuwa. Amma duk da haka wannan bai hana yawancin mutane kammala azumi cikin walwala da jin dadi ba. Haka kuma wannan sallah za ta baiwa 'yan uwa da aminan arziki da musulmi baki daya ziyartar juna domin sada zumunci da kuma neman gafara ga juna tare da fatan kwanciyar hankali da zaman lafiya a cikin kasar. (Maman Ada)