in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijer a shirye take ta kara yin hadin gwiwa da kasar Sin
2017-06-04 12:13:44 cri

Shugaban jamhuriyar Nijer Mahamadou Issoufoum ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take tayi hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni daban daban.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a lokacin da yake ganawa da mambar majalissar gudanarwar kasar Sin dake ziyara Wang Yong, wanda ya gabatarwa shugaban jamhuriya ta Nijer sakon fatan alheri daga shugaba Xi Jinping na kasar Sin.

Shugaban Issoufou ya bukaci mambar majalissar gudanarwar kasar Sin da ya gabatar da sakonsa na fatan alheri zuwa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping. Shugaban na Nijer ya bayyana farin cikinsa da kuma yabawa kasar Sin bisa irin taimakon da take ke baiwa Nijer wajen cigaban tattalin arziki.

Jamhuriyar Nijer tana matukar martaba kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin a fannoni da dama, in ji shugaba Issoufou.

A nasa bangaren, mambar majalissar gudanarwar kasar Sin ya bayyana Nijer a matsayin babbar aminiya ta hadin gwiwa don samun muriyar juna.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China