Da yake Karin haske game da yarjejeniyar da sassa biyu suka sanya hannu a birnin Nairobin kasar Kenya, wakiliyar shirin mai kula da yankin Afirka Juliette Koudenoukpo, ta bayyana cewa, shirin yana fatan taimakawa Jamhuriyar ta Nijar magance abubuwan dake gurbata muhalli wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula da tilastawa matasa yin kaura.
Koudenoukpo ta ce, karkashin wannan yarjejeniyar, shirin kare muhalli na MDD zai bunkasa hadin gwiwa da samar da taimako a fannonin da suka kula da harkokin kula da muhalli, sarrafa sinadarai da shara, da yaki da duk wani nau'i na gurbatar muhalli, ilimantar da jama'a game da matakan samarwa da kuma sarrafa abinci.
Jami'ar ta kuma bayyana cewa, ta hanyar wannan yarjejeniya za a bibiyi bangarorin da kasar ta Nijar ke da karfi da kuna inda take da nakasu, ta yadda za a fara daukar matakan raya tattalin arziki maras gurbata muhalli, da kafa wata hukuma, da bullo da tsare-tsaren da za su karfafa zuba jari a bangaren tattalin arzikin kasar.
A nasa jawabin ministan kare muhalli na Jamhuriyar Nijar Almoustapha Garba, ya bayyana cewa, gwamnati za ta yi amfani da wannan dama wajen kara fadada damammakin da take da su a bangaren tattalin arziki maras gurbata muhalli, domin samar da guraben ayyuka yi, a wani mataki na kauwa da hankalin matasa daga shiga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini.(Ibrahim)