in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude baje kolin na'urorin fasahohin zamani a birnin Shenzhen
2018-11-14 20:30:59 cri
Kimanin tawagogi 60 daga kasashe da yankuna 40, tare da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar bikin baje kolin na'urorin fasahohin zamani a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin.

An dai bude baje kolin na CHTF karo na 20 ne a Larabar nan, inda aka baje sabbin hajoji sama da 1,000, masu nasaba da na kwaikwayon tunanin bil Adama, da masu taimakawa wajen sarrafa kayayyakin masana'antu, da na tsimin makamashi, da na kare muhalli. Sauran sun hada da na bunkasa fasahar sadarwa, da na kyautata amfani da fasahohin sarrafa halittu, da makamashin da ake iya sabuntawa, da sabbin ababen sarrafawa. Sai kuma na fasahohin sararin samaniya, da hajojin da suka shafi sabbin fasahohin da aka gabatar a karon farko.

Gwamnatin birnin Shenzhen ce dai ta kirkiro bajen kolin na CHTF a shekarar 1999, a wani mataki na kokarin bunkasa tattalin arziki ta hanyar kirkire kirkire, tun daga wannan lokacin ne kuma ake ci gaba da gudanar da shi a duk shekara. A bana za a kwashe yini biyar ana gudanar da wannan baje koli.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China