in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna fasahohin zane na Afrika a Beijing
2018-10-28 16:15:22 cri

Dimbin zane-zane 'yan Afrika da Sinawa ne aka nuna a bikin nuna zane da aka yi a dakin karatu na kasar Sin a wannan makon.

Ma'aikatar wasanni da al'adu da fasaha ta kasar Kenya da hadin gwiwar kungiyar musayar al'adu ta Sin da Afrika da kuma dakin karatu na kasar Sin ne suka shirya bikin, wanda wani bangare ne na nune-nunen zanen kasar Sin da Afrika, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da kuma dandalin al'adu na kasar Sin da Afrika.

Sama da rabin zane-zane 110 da aka nuna, wadanda suka hada da zanen fenti da na alli da na sassaka ne masu zane sama da 40 na nahiyar Afrika suka yi, wadanda suka hada da 'yan kasar Kenya da Rwanda da Zimbabwe da Tanzania. Yawancin zanen Sinawa ya yi bayani ne kan shawarar Ziri Daya da hanya Daya da kuma rayuwar Afrika.

Daraktan sashen al'adu na ma'aikatar wasanni da al'adu da fasaha ta kasar Kenya, Kiprop Lagat, ya ce kasarsa ta samu dimbin moriya daga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Ya kuma bayyana fatan da wannan bikin, karin Sinawa za su yi sha'awar ziyartar Kenya domin su ga irin karamcin al'ummar kasar. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China