Shugaban kasar Sin ya mika sakon taya murnar cimma nasarar kera jirgin sama dake iya tashi daga kasa da kuma ruwa


A yau Asabar, jirgin saman kwana-kwana da bada agaji kan ruwa samfurin AG600 da kasar Sin ta kera, wanda ke iya tashi daga kasa da kuma kan ruwa, ya cimma nasarar gwajin tashi daga ruwa a filin jirgin sama na Zhanghe dake birnin Jingmen na lardin Hubei.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murnar cimma nasarar wannan aiki, yana mai bayyana shi a matsayin babban ci gaba da aka samu a fannin masana'antun jiragen sama na kasar. (Maryam)