in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kashe dala biliyan 28.74 wajen shigo da kayayyakin da suka shafi basirar dan adam a 2017
2018-11-06 16:27:26 cri
Mahukuntan kasar Sin sun fitar da wata kididdiga a yau Talata dake nuna cewa, kasar ta kashe kimanin dalar Amurka biliyan 28.74 wajen shigo da kayayyakin da suka shafi basirar dan adam a shekarar da ta gabata.

Alkaluman sun nuna cewa an samu karuwar adadin da kusan ninki 14 daga shekarar 2001, a lokacin da kasar ta shiga kungiyar ciniki ta duniya WTO, kamar yadda rahoton kididdigar da hukumar kula da shigo da kayayyaki zuwa kasar ta sanar wadda ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta fitar. Rahoton wanda aka wallafa a gefen bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na kasa da kasa a karo na farko dake gudana a birnin Shanghai.

A halin yanzu, kasar Sin tana halartar kusan dukkan muhimman tarurrukan kasa da kasa da suka shafi kayayyakin basirar dan adam, in ji rahoton. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China