in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci taron shugabannin RCEP karo na biyu
2018-11-15 10:59:04 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron shugabannin yarjejeniyar raya dangantakar abokantaka ta tattalin arziki a dukkan fannoni na yankin Asiya wato RCEP karo na 2, taron da ya gudana jiya a cibiyar shirya taruruka ta kasar Singapore, inda shugabannin kasashen kungiyar ASEAN 10 da na kasashen Koriya ta Kudu, Japan, Australia, New Zealand, da India suka halarci taron.

Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu an shiga muhimmin lokaci na shawarwari, ya kamata a ci gaba da hada kai don cimma yarjejeniyar a shekara mai zuwa, da kara samar da 'yanci da saukaka harkokin zuba jari da cinikayya da kokarin raya tattalin arzikin yankin, ta yadda za a samar da moriya ga al'ummomin kasa da kasa dake yankin.

Shugabannin dake halartar taron suna ganin cewa, a halin yanzu, tsananta ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da yaki da raya duniya bisa tsarin bai daya na kara tsananta. Ya kamata bangarori daban daban su kara hada kai don ganin an raya tattalin arziki bisa tsari na bai daya, da kiyaye ka'idojin kasa da kasa da yin ciniki cikin 'yanci bisa ka'ida.

A halin da ake ciki, cimma yarjejeniyar RCEP yana da matukar muhimmanci, kuma hakan zai taimakawa bangarori daban daban su kara yin imani da nuna goyon baya ga ra'ayin bangarori daban daban da yin ciniki cikin 'yanci, matakan da za su taimaka ga bunkasa tattalin arziki a yankin da ma raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China