in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya isa kasar Singapore
2018-11-12 20:13:32 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa kasar Singapore, domin fara ziyarar aiki, wadda ake fatan za ta share fagen bunkasa gudanar da cinikayya cikin 'yanci da hadin gwiwar yankin.

Yayin ziyarar ta sa, Li zai kuma halarci taron shugabannin kasashen kudu maso gabashin Asiya da kasar Sin karo na 21, da taron da kungiyar za ta yi da shugabannin kasashen Sin, da Japan, da Koriya ta arewa karo na 21, da kuma taron kolin kasashen gabashin Asiya karo na 13.

Ana dai kallo wannan ziyara ta firaministan Sin, a matsayin wani mataki na kasar Sin, game da yayata ra'ayin ci gaba, da cudanya tsakanin kasashe daban daban, da kuma bunkasa cinikayya cikin 'yanci. Hakan ya kuma yi daidai da manufar taron baje kolin hajojin da ake shigarwa kasar Sin da ya kammala a karshen mako, da ma manufar shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta halartar taron APEC dake tafe a Papua New Guinea, da kuma taron kungiyar G20 na kasar Argentina.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China