in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya halarci taron shugabannin kasashen ASEAN da na kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 21
2018-11-15 21:08:43 cri
Yau Alhamis, a kasar Singapore, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taro karo na 21, tsakanin shugabannin membobin kungiyar hadin-kan kasashen kudu maso gabashin Asiya ko kuma ASEAN a takaice, da takwarorinsu na kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu wato 10+3, inda shugabannin kasashe membobin kungiyar ASEAN guda 10, tare da shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu, da firaministan Japan Shinzo Abe suka halarci taron. Firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong ya jagoranci taron.

A cikin jawabin da ya gabatar, Li Keqiang ya ce, yayin da ake kokarin tinkarar rikicin kudi a nahiyar Asiya, da ma duk fadin duniya baki daya, kasashen kungiyar ASEAN gami da Sin da Japan da kuma Koriya ta Kudu sun taka muhimmiyar rawa. Har wa yau kuma, yayin da ra'ayin bada kariya ga harkokin cinikayya ke bazuwa a duniya, ya kamata kasashen 13 su ci gaba da kare tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, da gudanar da cinikayya cikin 'yanci. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China