in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika 6 sun kaddamar da makarantar nazarin harkokin shugabanci a Tanzania
2018-07-17 10:53:03 cri
Shugabannin jam'iyyu daga kasashen Afrika 6, sun aza harsashin gina makarantar nazarin harkokin Shugabanci a Tanzania.

Makarantar ta Julius Nyerere Leadership School da Jam'iyyu 6 na yankin kudancin Afrika suka assasa na da mazauni a yankin Kibaha dake da nisan kilomita 40 daga Dar es Salaam, babban birnin kasuwanci na kasar Tanzania.

Jam'iyyun 6 sun hada da Revolutionary party ta Tanzania da African National Congress ANC ta Afrika ta kudu da Mozambique Liberation Front Party da the People's Movement for the Liberation of Angola, da the SWAPO Party ta Namibia da kuma The Zimbabwe African National Union-Patriotic Front Zanu- PF.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi jinping, ya aike da sakon taya murna ga bukin kafa makarantar ta Julius Nyere.

Ya ce hada hannu wajen gina makarantar, muhimmin yunkuri ne da jam'iyyun 6 suka yi wajen karfafa kansu da inganta shugabanci da kuma taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kasashensu gaba.

A cewar Shugaban Tanzania John Magufuli, JKS ta mara baya ga jam'iyyun yankin kudancin Afrika 6, a fafutukarsu ta neman 'yanci tare kuma kulla kawance, yana mai cewa jam'iyyun 6 na godewa JKS bisa goyon bayan da take ci gaba da basu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China