in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
kamfanin kasar Sin ya ba wasu daliban kasar Kenya tallafin karatu a fannin shimfida layin dogo
2018-04-21 16:14:33 cri

Jimilar daliban kasar Kenya 40 ne za su fara karatu a Jami'ar Jiaotong ta birnin Beijing a karshen wannan watan, domin samun shaidar digiri a fannin injinya da ya shafi shimfida layin dogo, bisa tallafin da suka samu daga kamfanin gine-ginen tituna da gadoji na China wato CRBC a takaice.

Sakataren ma'aikatar sufuri na kasar James Macharia da Jakadan kasar Sin a Kenya Liu Xianfa da wasu manyan jami'an kamfanin CRBC na daga cikin wadanda suka halarci bikin yi wa daliban bankwana da ya gudana a birnin Nairobi.

James Macharia ya ce horar da matasan kasar kan fasahar shimfida layin dogo na zamani a babbar jami'ar kasar Sin, zai taimakawa kasar cike gibin da take da shi a bangaren fasaha wajen inganta harkar sufuri.

Tun a shekarar 2016 kamfanin CRBC ya ba matasa 100 tallafin karatu don samun shaidar digiri kan fannonin da suka shafi fasahohin shimfida layin dogo a jami'ar Jiaotong ta Beijing.

A nasa bangaren, Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasarsa za ta yayata fasahohinta domin kara zamanantar da bangaren layin dogo a Kenya, ta hanyar kafa kwalejojin bada horo a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China