in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Kenya sama da 600 sun zo Sin domin samun horo
2018-11-22 12:31:41 cri

Rahotanni daga ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya a jiya Laraba na cewa, a halin yanzu, Sin tana gudanar da ayyukan ba da horo ga ma'aikata a kasar Kenya cikin yanayi mai kyau. Kuma a shekarar bana, gaba daya akwai 'yan kasar Kenya guda 686 da suka zo kasar Sin domin samun horo, adadin da ya karu da kaso 22%, idan aka kwatanta da na shekarar bara.

Ban da haka kuma, dalibai guda 61 daga cikinsu sun sami kyautar kudin karatu, wanda ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta samar musu, wadanda suka shiga jami'o'in Tsinghua da Tongji da dai sauransu domin kara karatu.

A gun taron karawa juna sani tsakanin daliban da suka samu horo a kasar Sin da aka yi a wannan rana, mashawarcin jakada kan harkokin kasuwanci da tattalin arziki na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Kenya Guoce ya bayyana cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara ba da horo ga 'yan kasar Kenya, domin biyan bukatun kasar wajen neman ci gaba. Haka kuma, za ta sabunta hanyoyin ba da horo ga dalibai, ta yadda za a karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

A nasa bangare kuma, shugaban cibiyar harkokin kwadago ta ma'aikatar harkokin ba da hidima, matasa da jinsi ta kasar Kenya Dennis Mutahi, ya nuna godiya ga taimakon da kasar Sin ta yi wa kasar Kenya. Ya ce, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga kasar Kenya a fannin ba da horo ga ma'aikata. Kuma ma'aikatan gwamnatin kasar Kenya sun karu sosai bisa horon da aka ba su, da kuma karatun da suka yi a yayin tarukan karawa juna sani, lamarin da ya karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen Sin da Kenya kwarai da gaske a fannonin ba da ilmi, da fasahohi, da kuma cinikayya da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China