in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin dake Kenya ya samar wa kasar na'urorin aikin jinya domin raya harkokin kiwon lafiyar mata da yaran kasar
2018-03-09 10:48:16 cri
An yi bikin raya abota tsakanin Sin da Afirka jiya Alhamis, a fadar shugaban kasar Kenya dake birnin Nairobi, inda kasar Sin ta samar wa Kenya na'urorin aikin jinya.

Jakadan kasar Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa da uwargidan shugaban kasar Kenya Margaret Kenyatta sun halarci bikin.

Har ila yau, bikin da ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya ya shirya, ya samun halartar kamfanonin Sin da dama, ciki har da kamfanin Weigao. Kuma an shirya samar wa Asusun "Beyond Zero" da ofishin uwargidan shugaban kasar Kenya ya kafa, wasu gadajen tiyata da akwatunan kiyaye zafin jikin jarirai da dai sauran na'urorin aikin jinya, wadanda gaba daya kudinsu ya kai dallar Amurka dubu 130, domin taimaka wa kasar Kenya kan ayyukan kiwon lafiya, musamman ma a fannin kiwon lafiyar mata da yara. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China