in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CMG ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da RTP
2018-12-06 10:29:58 cri
Jiya Laraba, Babban Gidan Rediyo da Talibijin na kasar Sin wato CMG, ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da Babban Gidan Rediyo da Talibijin na kasar Portugal wato RTP. Bangarorin biyu za su fara hadin gwiwa a fannonin musayar labarai, da mu'amalar ma'aikata, da kuma yin shirye-shirye da dai sauransu.

Bisa yarjejeniyar da suka kulla, an ce, cikin shekaru uku masu zuwa, bangarorin biyu za su sa kaimi ga gidajen rediyo da gidajen talibijin dake karkashin jagorancinsu, su yi hadin gwiwar watsa labarai bisa ka'idar nuna gaskiya, kuma bisa dukkan fannoni, domin karfafa fahimtar juna da zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu. (Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China